Spaniya : Faransa Da Jamus Sun Jadadda goyan Baya Ga Gwamnatin Madrid
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Faransa Emanuel, sun jadadda goyan bayansu ga gwamnatin Madrid kan rikicin yankin Cataloniya, a yayin da takwaransu na Biegium ke kiran a kai zuciya nesa.
Wannan kiran dai na zuwa ne bayan da wa'adin da gwamnatin Madrid ta baiwa jagoran 'yan a ware na Katoniya akan ya bayyana matsayinsa kan zaben raba gardama na yankin a yau Al'hamis.
Shugaban gwamnatin Spaniya Mariano Rajoy wanda ke iya daukan mataki na soke cin gashin kan da yankin na Kataloniya ke da shi, ya isa a birnin Brussuls yau a taron kasashen turai inda zai gana da takwarorinsa 27.
Ko da yake rikicin da ya biyo bayan zaben raba gardama na yankin Kataloniya baya daga cikin ajandar taron, aman ya dau hankalin mahalarta taron ba kadan ba.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce suna goyan bayan gwamnatin Spaniya, kuma suna fatan za'a samu mafita akan rikicin kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Shi kuwa a nasa bangare Emanulle Maccron na Faransa cewa ya yi, kasashen turai zasu aikewa da sakon hadin kai ga kasar ta Spaniya.