Pars Today
Wani sabon sabani tsakanin kasashen Masar da Turkiyya ya sake kunno kai bayan da Masar ta sake samun nasarar gano yankuna masu dauke da iskar gas da man fetur a kusa da kan iyakarta da kasar Cyprus.
Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya kammala gajeren ran gadin da ya kaddamar a wasu kasashen nahiyar AFrika.
Shugaban kasar Turkiyya ya bayyana jin dadinsa da yadda ake ci gaba da samun bunkasar alaka tsakanin kasarsa da kasashen nahiyar Afrika.
Daruruwan mutanen kasar Siriya ne suka gudanar da jerin gwano a garin Afrin na kasar don nuna farin cikinsu da kuma yin maraba da dakarun da suke goyon bayan gwamnatin kasar wadanda suka shigo garin da nufin ba su kariya daga ci gaba da hare-haren da sojojin Turkiyya suke yi wa garin.
Sojojinn kasar Turkiya sun yi harbi kan sojojin sa kai masu goyon bayan kasar Siria wadanda suka shiga yankin Afrin a jiya Talata.
Tashar talabijin din al-mayadden mai watsa shirye-shiryenta daga Lebanon ta ce; Mayakan sun shiga cikin garin na Afrin ta mashigar al-ziyara a kauyen Nubbal.
Duban 'yan kasar Siriya mazauna garin Afrin dake arewacin kasar sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da hare-haren da dakarun saman turkiya ke kaiwa kan al'ummar yankin.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya bayyana cewa farmakin da Turkiyya ke kaiwa kan mayakan Kurdawa a arewacin Siriya, ya raunana yakin da ake da kungiyar 'yan ta'adda ta IS.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta yi gargadin cewa; Sabon matakin mahukuntan Turkiyya kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen Masar da Cyprus a yankin tekun mediterraniya yana matsayin kokarin yin zagon kasa ne ga harkar tattalin arzikin Masar.
Dangantaka tsakanin kasashen Masar da Turkiya ta yi tsami a cikin yan kwanakin nan, saboda sanin iyakokin da kowanne daga cikin yake mallaka a tekun Mediterranean .