Pars Today
A Labanon, daruruwan Kurdawa ne suka gudanar da wata zanga-zanga yau Litini gaban ofishin jakadancin Amurka dake Beirut, domin yin allawadai da farmakin da Turkiyya ke ci gaba da kaiwa a yankin Afrin na Siriya.
majiyar Kurdawa ce ta sanar da kashe sojojin Turkiya biyar tare da jikkata wasu a kauyen ALi-Kara, ayankin Afrin.
A ci gaba da farmakin da take kaiwa a yankunan Kurdawan na Siriya, Turkiyya ta sake aikewa da wani ayarin motocin soji a yankin Anadan.
Jiragen saman yakin gwamnatin Turkiyya sun yi luguden wuta kan kauyukan da suke garin Afrin a lardin Halab na kasar Siriya, inda suka kashe fararen hula akalla goma sha uku.
Mayakan kungiyar Kurdawan Syria wacce aka fi sani da YPK sun sanar da kame sojojin Turkiya 16 a yau juma'a.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan, na Turkiyya ya ce kasarsa za ta ci gaba da farmakin da take kaiwa kan mayakan Kurdawa na (YPG) dak take dangantawa da 'yan ta'ada a yankin Afrin.
Kakakin Rundunar tsaron kasar Libiya ya zargi gwamnatin Turkiya da hannu a hare-haren ta'adancin da aka kai birnin Benghazi.
Ministan harakokin wajen Masar ya bayyana ayyukan sojan Turkiya a garin Afrin na kasar Siriya a matsayin barazana a kokarin da ake yi na magance rikicin kasar.
Mayakan Kurdawan a yammacin gundumar Afirn sun sanar da kwace tuddai masu muhimmanci da sojojin Turkiya suka kama a baya.
Rundinar sojin Turkiyya ta kai hare-haren sama a kan wasu sansanonin mayakan Kurdawa na PKK a arewacin Iraki.