Syria: Mayakan Kurdawa Sun Kama Sojojin Turkiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27667-syria_mayakan_kurdawa_sun_kama_sojojin_turkiya
Mayakan kungiyar Kurdawan Syria wacce aka fi sani da YPK sun sanar da kame sojojin Turkiya 16 a yau juma'a.
(last modified 2018-08-22T11:31:20+00:00 )
Jan 26, 2018 19:19 UTC
  • Syria: Mayakan Kurdawa Sun Kama Sojojin Turkiya

Mayakan kungiyar Kurdawan Syria wacce aka fi sani da YPK sun sanar da kame sojojin Turkiya 16 a yau juma'a.

Mai magana da yawun mayakan Ahmad Shauki ne ya bada labarin kame sojojin Turkiya, da ya ce ya faru ne a yankin Jindires. Har ila yau Shauki ya kuma kara da cewa a yayin gumurzun da suka yi da sojojin na Turkiya 4 daga cikin mayakansu sun bace.

Wata majiyar ta kungiyar YPK ta ce; kungiyar tasu tana kare yankin Afrin ne daga hare-haren Da'esh, kuma yankin wani sashe ne na kasar Syria. Kurdawan sun zargi Turkiya da kokarin balle yankin daga karkashin Syria.

Tun a ranar asabar din da ta gabata ne dai Turkiya ta fara kai hari a yankin Afrin na kasar Syria domin kawar da abinda ta kira hatsarin 'yan ta'addar kungiyoyin Kurdawa.

Syria ta yi Allah wadai da harin na sojojin Turkiya tare da bayyan hakan a matsayin keta hurumin kasar syria