Turkiyya Ta Kai Hari Kan Sansanonin Kurdawan Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27531-turkiyya_ta_kai_hari_kan_sansanonin_kurdawan_iraki
Rundinar sojin Turkiyya ta kai hare-haren sama a kan wasu sansanonin mayakan Kurdawa na PKK a arewacin Iraki.
(last modified 2018-08-22T11:31:19+00:00 )
Jan 23, 2018 11:18 UTC
  • Turkiyya Ta Kai Hari Kan Sansanonin Kurdawan Iraki

Rundinar sojin Turkiyya ta kai hare-haren sama a kan wasu sansanonin mayakan Kurdawa na PKK a arewacin Iraki.

Wadannan hare-hare na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga kwana na hudu da Turkiyyar ke kai hari kan Kurdawa a yankin Afrin na Siriya.

Wata sanarwa da rundinar sojin Turkiyyar ta fitar a yau ta ce, an kai harin ne a sansanonin Kurdawan na PKK dake shirin kai hari wa sansanonin sojin Turkiyya a iyaka da Irakin.

Sanarwar ta ce an lalata wuraren buya na mayakan da kuma makaman yaki a harin da aka kai a yankin Zab dake arewacin kasar ta Iraki.