Syria: An kashe Sojojin Turkiya Da Dama A yanain Afrin
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27903-syria_an_kashe_sojojin_turkiya_da_dama_a_yanain_afrin
majiyar Kurdawa ce ta sanar da kashe sojojin Turkiya biyar tare da jikkata wasu a kauyen ALi-Kara, ayankin Afrin.
(last modified 2018-08-22T11:31:22+00:00 )
Feb 03, 2018 18:57 UTC
  • Syria: An kashe Sojojin Turkiya Da Dama A yanain Afrin

majiyar Kurdawa ce ta sanar da kashe sojojin Turkiya biyar tare da jikkata wasu a kauyen ALi-Kara, ayankin Afrin.

Majiyar ta ci gaba da cewa an yi bata-kashi ne a tsakanin mayakan Kurdawan da kuma sojojin Turkiya, kuma baya ga kashe biyar daga cikinsu, an jikkata wasu shida.

Shugaban cibiyar watsa labaru na mayakan Kurdawa, Mustafa Bali ya ce; Turkawan suna kokarin kawar da hankali mutane ne daga kan shan kashin da suke yi a yankin na Afrin.

Makwanni biyu kenan da sojojin na Turkiya suka kutsa cikin kasar Syria domin fada da Kurdawa, sai dai har yanzu suna fuskantar turjiya daga mayakan Kurdawa.