Pars Today
Zanga-Zangar da mutanen arewacin kasar Morocco suke yi tun ranar Alhamis da ta gabata ya sanya yan sandan kasar suka yi kokarin dakatar da ita da karfi, wanda ya kai sa insa da masu zanga-zangar.
Ministan tsaron kasar Kamaru ya bada sanarwan cewa na kama sojojin kasar 30 wadanda suka toshe tituna a wani gari da suke aiki a arewacin kasar a cikin wannan makon tare da bukatar a biyasu karin kudade don ayyukan da suke yi.
Gungun 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a kasar Siriya sun harba makamai masu linzami kan yankunan da suke lardin Dire-Zur na kasar Siriya da ke kusa da kan iyaka da kasar Iraki, inda suka kashe fararen hula.
Dubun dubatan mutanen kasar Afirka ta Kudu ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin Pretoria suna masu kiran shugaban kasar Jacob Zuma da ya sauka daga karagar mulkin kasar.
Ministan harkokin wajen kasar Venezuela Delcy Rodriguez ya zargi wasu kafafen yada labarai a kasar da kuma na kasashen waje wajen tallafawa yan adawar kasar da kuma rashin fadar hakikanin abinda ke faruwa a kasar a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Yan adawar Venezuala sun fara gudanar da wani gagarumin gangami na sai baba ta gani a sassa daban daban na kasar domin ganin sun tursasa wa gwamnatin kasar ta amsa bukatarsu ta gudanar da zabe kafin wa'adinsa.
Daruruwann 'yan kasuwa a birnin Kampala fadar mulkin kasar Uganda sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin amincewarsu kan yadda baki 'yan kasar China suka mamaye musu harkokin kasuwanci.
Shugaban Kasar Amurka ya soki Siyasar harakokin wajen Gwamnatin da ta gabata
Majiyar tsaron Venezuala ta sanar da cewa: Zanga-zangar nuna kiyayya ga gwamnatin kasar ta fara kamari a yankunan da suke kewaye da birnin Caracas fadar mulkin kasar.
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya zargin masu zanga-zangar da suke kiransa da yayi murabus daga mukaminsa sakamakon gazawar da suka ce yayi wajen kyautata yanayin kasar a matsayin 'yan nuna wariyar launin fata.