Shugaba Trump Ya Soki Gwamnatin Barak Obama
Shugaban Kasar Amurka ya soki Siyasar harakokin wajen Gwamnatin da ta gabata
A cikin wani jawabi da ya gabatar yau Litinin albakacin cikar Kwanaki 90 na Gwamnatinsa, Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana rashin nasarar da Gwamnatin Barak Obama ta samu a harakokin siyasar wajen Amurka cikin shekaru takwas da suka gabata.
A yayin da yake sukar Siyasar harakokin wajen Gwamnatin Obama, Shugaba Trump ya ce a zamanin milkin Barak Obama ne Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un ya samu damar yin gwajin makamai masu Linzami.
Yayin da ya koma kan jaridun kasar Mista Trump ya ce kafafen yada labarai masu tsauri ba wai kafafen yada labarai na gaskiya ba sun munana a yayin zaben kasar, domin dukkanin labaran da suka shafi zabe sun yi mumunar murguda gaskiyarsa kuma dole mu tilasta su, su kasance masu fadar gaskiya.
Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da Shugaba Trump ke sukar kafafen yada labaran kasar ta Amurka tun bayan da ya dare kan karagar milkin kasar.