-
Masar: Martanin Cibiyar Darul Fatawa Kan Kalubalantar Kur’ani Da Faransawa 300 Suka Yi
Apr 26, 2018 02:08Khalid Umran babban sakataren cibiyar darul fatawa ta kasar Masar, ya bayyana kiran da wasu fitattun Faransawa 300 suka yi na a cire wasu ayoyin kur’ani da cewa aiki ne na shaidanci.
-
Najeriya: Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Shugaba Buhari Domin Ya Bayyana A Gabanta
Apr 26, 2018 02:08Majalisar wakilan Najeriya ta aike da sakon gayyata ga shugaba Buhari domin ya bayyana a gabanta, da nufin tattaunawa tare da shi kan matsalolin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a wasu yankuna na kasar musamman a jahar Benue.
-
Afirka Ta Kudu: Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Tsarin Albashi Mafi Karanci
Apr 26, 2018 02:07Gamayyar kungiyoyin kwadago a kasar Afirka ta kudu na gudanar da gangami da jerin gwano a biranan kasar, domin nuna rashin amincewa da tsarin albashi mafi karanci.
-
Wani Mai Gabatar Da Kara Na Soja A Libya Ya Tsere Daga Hannun Masu Garkuwa Da Shi
Apr 25, 2018 14:35Wani mai gabatar da kara soja a kasar Libya tare da masu tsaronsa biyu sun tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su sun tsaresu na tsawon kimani wata guda.
-
Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Ya Yi Watsi Da Kiraye-Kirayen Yan Adawa Na Ya Sauka
Apr 25, 2018 14:34Shugaban kasar Sudan ta Kudu Silva Kiir ya yi watsi da kiraye-kirayen yan adawar kasar na ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar idan yana son zaman lafiya ya dawo kasar.
-
Rwanda : An Gano Gawawwakin Mutane 200 A Wani Makeken Kabari
Apr 25, 2018 06:27A Rwanda an gano wani makeken kabari dauke da gawawwakin mutane sama da 200, da ake kyautata zaton na lokacin kisan kiyashin kasar ne.
-
Majalisar Dattawan Nijeriya Ta Kafa Kwamitin Binciken Sace Sanda Ikon Majalisar Da Aka Yi
Apr 25, 2018 00:57Majalisar dattawan Nijeriya ta sanar da kafa wani kwamiti da zai binciko hakikanin abin da ya faru biyo bayan sace sandan ikon majalisar da wasu 'yan daba suka yi a kwanakin baya lamarin da ya janyo kace-nace a majalisar da kuma tsakanin 'yan Nijeriyan.
-
Madugun 'Yan Adawan Kongo Ya Musanta Cimma Yarjejeniya Da Shugaba Kabila
Apr 25, 2018 00:56Madugun 'yan adawan kasar Demokradiyyar Kongo, Felix Tshisekedi, yayi watsi da wasu labarai da ke cewa yana shirin cimma yarjejeniya da shugaban kasar ta Kongo Joseph Kabila wanda ke fuskantar matsin lambar ya sauka daga karagar mulki.
-
An Kashe Wani Matashi A zanga-Zangar Da Ake Yi A Afirka Ta Kudu
Apr 24, 2018 14:45Jami'an 'yan sanda a kasar Afirka ta kudu sun sanar kashe wani matashi a zanga-zangar da ake yi a wasu yankunan kasar, domin nuna rashin amincewa da barna da dukiyar kasa.
-
Habasha Ta Bukaci Birtaniya da Ta Mayar Mata Da Kayan Tarihinta Da Ta Wawushe
Apr 24, 2018 14:44Jami'an gwamnatin kasar Habasha sun bukaci Birtaniya da ta mayarwa kasarsu kayan tarihi da ta wawushe tun a llokacin mulkin mallaka, da aka saka su a gidan tarihi na Virctoria and Albert da ke London.