Rwanda : An Gano Gawawwakin Mutane 200 A Wani Makeken Kabari
Apr 25, 2018 06:27 UTC
A Rwanda an gano wani makeken kabari dauke da gawawwakin mutane sama da 200, da ake kyautata zaton na lokacin kisan kiyashin kasar ne.
Kungiyar wandada suka tsira ta Ibuka ta kasar Rwanda, ta ce sama da gawawwaki 200 aka tonu daga wani kabari na bai daya, na wadanda kisan kiyashin kasar na 1994 ya rutsa da su.
Shugaban kungiyar Theogene Kabagambire, ya ce an ajiye gawawwakin da aka tono daga kabarin mai zurfin mita 30 na yankin Rusororo na Lardin Gasabo a ofisoshin lardin, inda ake jiran yi musu jana'izar da ta dace.
Ya kara da cewa, akwai wasu kaburbura 3 na bai daya da ba a kai ga tonowa ba a wannan yankin.
Tags