Najeriya: Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Shugaba Buhari Domin Ya Bayyana A Gabanta
Majalisar wakilan Najeriya ta aike da sakon gayyata ga shugaba Buhari domin ya bayyana a gabanta, da nufin tattaunawa tare da shi kan matsalolin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a wasu yankuna na kasar musamman a jahar Benue.
Jaridar Vanguard da ake bukagawa a Najeriya ta bayar da rahoton cewa, majalisar wakilan ta aike da sakon gayyatar ne sakamakon korafe-korafen da suka yi yawa kan yadda rikice-rikice ke ta lakume rayukan jama'a a jahar Benue musammana cikin 'yan kwanakin nan.
Baya ga haka kuma ire-iren wadannan rikice-rikice na makiya da manoma suna faruwa awasu jahohi yankunan arewacin kasar, da suka hada da Kaduna, Filato, Taraba da kuma Nasarawa, kamar yadda kuma a jahar Zamfara ma wasu 'yan bindigar suka addabi jama'a, rikice-rikicen da 'yan majalisar suke cewa gwamnati ta kasa shawo kansu, yayin da gwamnatin take cewa tana yin iyakacin kokarinta kan batun.
Wasu daga cikin 'yan majalisar sun bukaci da sauke dukkanin manyan hafsoshin sojin kasar da ma manyan jami'an tsaro sauran bangarorin, bisa a bin da suka kira kasa tabbatar da tsaro ga 'yan Najeriya.