-
Allah Yayi Wa Tsohon Shugaban Kasar Sudan Rasuwa
Oct 19, 2018 06:49Rahotanni daga kasar Sudan sun bayyana cewar Allah Ya yi wa tsohon shugaban kasar, Janar Abdulrahman Suwar Al-Dahab rasuwa yana dan shekaru 83 a duniya.
-
An Fafata Tsakanin Tsakanin Sojojin Mali Da Yan Bindiga A Arewacin Kasar
Oct 19, 2018 03:19Fada ta barke tsakanin sojojin kasar Mali da yan ta'adda dauke da makamai a arewacin kasar Mali a ranar laraba da ta gabata.
-
Majalisar Dokokin Kasar Sudan Ta Kudu Ta Amince Da Yerjejeniyar Sulhu Da Yan Tawayen Kasar
Oct 19, 2018 03:13A jiya Alhamis ce majalisar dokokin kasar Sudan ta Kudu ta amince da yarjejeniyar sulhu wacce gwamnatin kasar ta cimma da yan tawaye kimanin wata guda da ya gabata.
-
Ana Saran Wani Dan Kasar Algeriya Ne Zai Maye Gurbin De Mistura A Aikin Zaman Lafiya A Siriya
Oct 19, 2018 03:10Kafafen yada labarai na kasar Algeriya da kuma na yankin gabas ta tsakiya da dama sun bayyana cewa tsohon ministan harkokin wajen kasar Algeriya ne zai maye gurbin Staffan De Mistura a aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar Siriya.
-
Majalisar Tattalin Arziki A Najeriya Ta Gudanar Da Taro Ba Tare Da Tattauna Batun Albashi Mafi Karanci Ba
Oct 19, 2018 03:04Majalisar tattalin arzikin a tarayyar Najeriya ta gudanar da taro a jiya Alhamis karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo amma ba tare tattauna batun albashi mafi karanci ba.
-
Zaben 2019: Buhari Da Jami'an Tsaro Sun Koka Kan Yadda Yan Siyasa Suke Tattara Makamai Kafin Zabe
Oct 19, 2018 02:58Shugaba muhammadu Buhari a tarayyar Najeriya tare da manya manyan jami'an tsaron kasar sun nuna damuwarsu kan yadda yan siyasa suke tara makamai kafin zaben mai zuwa.
-
Gabon : 'Yan Adawa Sun Ce An Tabka Magudi A Zaben 'Yan Majalisa
Oct 18, 2018 11:52Manyan jam'iyyun adawa a Gabon sun yi zargi jam'iyya mai mulki a kasar da tabka magudu a zaben 'yan majalisar dokokin dana wakilan kananan hukumomin kasar da aka kada kuri'arsa a ranar 6 ga watan Oktoban nan.
-
INEC : Jam'iyyu 17 Kacal Suka Mika Sunayen Yan Takararsu
Oct 18, 2018 08:47Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa jam'iyyu 17 ne kadai daga cikin jam'iyyu 91 suka bada sunayen yan takararsu na zaben shekara ta 2019 a zuwa yau 18 ga watan Octoba.
-
Najeriya : NLC Za Ta Gudanar da Zama Kan Batun Karin Albashi
Oct 18, 2018 02:22Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya, ta sanar da cewa a yau Alhamis mambobinta za su gudanar da wani zama domin tattauna batun karin albashin ma'aikata mafi karanci.
-
Wasu 'Yan Majalisun Dokokin Aljeriya Sun Bukaci Shugaban Majalisar Da Ya Yi Murabus
Oct 17, 2018 15:26Wasu 'yan majalisun dokokin Aljeriya sun bukaci shugaban Majalisar kasar da ya sauka daga kan mukaminsa.