Allah Yayi Wa Tsohon Shugaban Kasar Sudan Rasuwa
(last modified Fri, 19 Oct 2018 10:19:41 GMT )
Oct 19, 2018 10:19 UTC
  • Allah Yayi Wa Tsohon Shugaban Kasar Sudan Rasuwa

Rahotanni daga kasar Sudan sun bayyana cewar Allah Ya yi wa tsohon shugaban kasar, Janar Abdulrahman Suwar Al-Dahab rasuwa yana dan shekaru 83 a duniya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Sudan din (SUNA) ya ba da labarin cewa a jiya Alhamis ne tsohon shugaba Abdulrahman Suwar Al-Dahab ya rasu a wani asibitin soji da ke birnin Riyadh na kasar Saudiyya ba tare da yin wani karin bayani ba.

Janar Abdulrahman Suwar Al-Dahab ya dare karagar mulkin kasar Sudan din bayan juyin mulkin soji da yayi wa shugaban kasar Sudan din na lokacin Ja'afar Numeiri.

Bayan saukarsa daga karagar mulkin kasar Sudan,  Janar Suwar al-Dhahab ya ci gaba da gudanar da ayyukansa karkashin kungiyar nan ta Islamic Call Organization.