Mar 18, 2019 05:13 UTC
  • Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati A Sudan

Dubun dubatan al'ummar kasar Sudan Ne Suka gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a yankuna da dama na kasar

A yayin da gwamnatin Sudan ta sanar da karbo bashi na dala miliyan 300 da nufin magance matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, a jiya Lahadi dubun dubatan 'yan kasar ne suka gudanar da zanga-zangar neman shugaba Omar al-bachir ya yi murabus a birnin Khartum da wasu biranan kasar.

Duk da irin matakan da gwamnatin Sudan din ke dauka na ganin a samu saukin rayuwa a kasar, masu adawa da shugaba Al-bachir sun dage a kan lalle sai ya yi murabus.

Tun a ranar 19 ga watan Dicembar 2018 din da ta gabata ce, al'ummar kasar sudan suka fara gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin kayan masarufi, musaman ma man fetir da biredi da ya kasance abincin yau da kulun na dukkanin al'ummar kasar.

A shekarun baya-bayan nan ba a taba ganin irin wannan zanga-zanga ba a kasar ta Sudan da ta yi sanadiyar salwanta rayukan mutum 40 a kasar

Tun a shekarar 1993 ne shugaba Omar al-Bachir ke rike da madafun ikon kasar ta Sudan, kuma bisa tsarin kundin milkin kasar, a shekarar 2020 ne wa'adin milkinsa zai kawo karshe.

Tags