Pars Today
Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Khaminae ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amarka tana taimakawa gwamnatin kasar Saudia a ta'asar da take aikatawa a kasar Yemen.
A dazu-dazun nan ne komitin tsaro na MDD ya fara zama don sauraron rahoton dangane da yerjejeniyar Nukliyar kasar Iran, wacce kudurin MDD ta 2231 ta maida ita doka.
Shugaban kasar Iran Hasan Rouhani ya bayyana goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga tattaunawar sulhun kasar Yemen yana mai cewa a halin yanzu 'yan mamaya sun fahimci cewa yin sulhu da al'ummar Yemen shi ne kawai damar da suke da shi.
Shugaban Jamhuriya Musulinci ta Iran, Dakta Hassan Rouhani, ya soki matakan Amurka na kakaba wa kasarsa takunkumi, yana mai bayyana yunkurin a matsayin ta'addanci kan tattalin arziki.
'Yan sanda a Iran, sun cafke mutum 10, a ci gaba da binciken da ake bayan harin ta'addancin da ya janyo shahadar 'yan sanda biyu a yankin kudu maso gabashin kasar a ranar Alhamis data gabata.
Rahotanni daga kasar Jamus na cewa, gwamnatocin kasashen kasar ta Jamus da kuma Faransa, sun cimma matsaya kan samar da hanyar ta'ammuli da kudade tare da kasar Iran.
Ofishin jakadancin Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana mamayar da 'Isra'ila' ta yi wa yankunan Palastinawa a matsayin tushen rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya.
Ministan man fetur na kasar Iran Namdar Zangeneh ya bayyana cewar a halin da ake ciki Iran ba za ta taba amincewa da rage yawan man fetur din da take fitarwa a kowace rana ba.
Rahotanni daga garin Chabahar da ke Kudu Maso Gabashin kasar Iran sun bayyana cewar mutane uku sun yi shahada kana wasu kuma da dama sun sami raunuka sakamakon wani harin ta'addancin da aka kai kusa da helkwatar 'yan sandan da ke garin da safiyar yau Alhamis.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba tattaunawa da wata kasa dangane da makamanta na kariya ba.