Dec 11, 2018 16:21 UTC
  • Iran Ta Sanar Da Goyon Bayanta Ga Shirin Sulhun Kasar Yemen

Shugaban kasar Iran Hasan Rouhani ya bayyana goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga tattaunawar sulhun kasar Yemen yana mai cewa a halin yanzu 'yan mamaya sun fahimci cewa yin sulhu da al'ummar Yemen shi ne kawai damar da suke da shi.

Shugaban kasar  ta Iran ya  bayyana hakan ne a karshen zaman da shugabannin bangarori uku na gwamnatin kasar Iran suka gudanar a yau Talata inda ya ce: A halin yanzu alamu suna kara bayyana da suke nuni da komawa zuwa ga tabbatar da sulhu a kasar Yemen, yana mai cewa tun da jimawa Iran tana goyon bayan tabbatar da  sulhu tsakanin bangarori da ba sa ga maciji da juna a kasar Yemen.

Shugaba Rouhani ya ce abin da ke faruwa a kasar Yemen ya sanya wadanda suke son mamayye kasar fahimtar cewa sulhu da zaman lafiya da al'ummar Yemen ita ce kawai mafita a gare su.

Shugaban na Iran yana magana ne dangane tattaunawar sulhun kasar Yemen da ke gudana a kasar Sweden karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya tsakanin bangaren 'yan kungiyar Ansarullah da bangaren da ke goyon bayan tsohuwar gwamnatin kasar.

A wani bangare na jawabin nasa, shugaba Rouhani ya ce kasar Amurka ta gaza wajen hana Iran sayar da man fetur dinta a kasuwannin duniya tun bayan da ta sake kakabawa Iran takunkumi bayan ta fice daga yarjejeniyar nukiliyan da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya ciki kuwa har da Amurkan a shekara ta 2015.

 

Tags