Mar 04, 2019 05:15 UTC
  • Huthy: HKI Tana Cikin Masu Yakar Kasar Yemen

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik Badurddin al-Huthy, ya ce; Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana cikin masu yakar mutanen Yemen, ya kuma kara da cewa adawar da take wa mutanen kasar a fili take, musamman a kafafen watsa labaranta

A cikin wa ni jawabi da ya gabatar wanda aka watsa ta tashar talabijin ta Almasiriyya, shugaban na kungiyar Ansarullah ya kara da cewa; Nuna adawar da ake yi wa Hizbullah, da kungiyoyin gwgawarmayar Palasdinawa, tushen su shi ne haramtacciyar kasar Isra’ila.

Sayyid Abdulmalik al-Huthy ya kuma yi tsokaci akan taron birnin Warsaw na kasar Poland inda ya ce manufarsa it ace kulla alaka a tsakanin larabawa da haramtacciyar kasar Isra’ila.

Har ila yau jagoran kungiyar ta Ansarullah, ya jinjinawa al’umar kasar ta Yemen wadanda su ka gudanar da gangami na nuna kin amincewa da taron na birnin Warsaw.

 

A wani sashe na jawabin jagoran kungiyar ta Ansarullah ya kuma kara da cewa; Taron na kasar Poland ya tona asirin masu son kulla alaka da  Sahyoniyawa da kuma yadda suke adawa da duk wanda bai laminta da yahudawan ba.

 

Tags