MDD: Kashi 80% Na Mutanen Kasar Yemen Na Bukatar Taimakon Gaggawa.
Majalisar dinkin duniya ta bada sanarwan cewa matsalar abinci na kara tsanani a kasar Yemen
kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto hukumar bada agajin gaggawa ta MDD tana fadara haka a yau Akhamis. Ta kuma kara da cewa yakin da ake yi a kasar Yemen ya janyo fari a kasar kuma yanayin rayuwa a kasar yana kara tabarbarewa.
Bayanan hukumar ta agajin gaggawa sun kara da cewa matsalar rashin abinci ko yunwa ya shafi kusan kashi 80 na mutanen kasar, wato kimanin mutane miliyon 24 kenan.
Gwamnatin kasar Saudia tare da kawayenta na kasashen Larabawa wadanda suka hada da UAE, tare da taimakon wasu kasashen yamma sun farawa kasar Yemen da yakin watan Maris na shekara ta 2015 da nufin maida tsohon shugaban kasar ta Yemen Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar.
Ya zuwa yanzu dai mutanen kasar kimani dubu 16 suka rasa rayukansu sanadiyar ruwan bomabomai wadanda wadannan kasashe suka jafa a kan mutanen kasar.