Feb 09, 2019 05:16 UTC
  • Jiragen Yakin Kawancen Saudiya Sun Yi Lugudar Wuta A Babban Birnin Kasar Yemen

A jijjifin safiyar yau assabar jiragen yakin kasar Saudiya sun yi lugudar wuta a Sana'a babban birnin kasar yemen.

Kamfanin dillancin labaran Meher ya habarta cewa a jijjifin safiyar yau assabar an ji kara mai tsanani sanadiyar fashewar wasu ababe yayin ruwan bama-bamai da jiragen yakin kawancen saudiya suka yi a sana'a babban birnin kasar yemen.

Saudiya ta yi da'awar cewa ta kai harin ne kan wasu ma'ajiyar makamai da sansanin sojan kasar Yemen dake birnin na Sana'a.

Rahoton ya ce har yanzu jiragen yakin kawancen saudiya na shawaki a sararin samaniyar birnin sana'a.kuma ya zuwa yanzu ba a bayyana irin hasarar da wannan mumunan harin wuce gona da iri na kawancen saudiyan ya janyo ba.

Tun a watan Maris din 2015 ne kasar Saudiya tare da cikekken goyon bayan Amurka da hadaddiyar daular larabawa gami da wasu kasashe ta kaddamar da yakin wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen tare da killace kasar ta kasa da sama da ruwa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar yamaniyar sama da dubu 16 da jikkata wasu dubai na daban tare kuma da raba wasu milyoyi da mahalinsu.

Bayan kwashe kusan shekaru, ya zuwa yanzu dai kasar Saudiya ta kasa cimma manufofinta a kasar ta yemen, sakakon juriya da kuma gwagwarmayar al'ummar kasar Yemen.

Tags