Mar 13, 2019 16:47 UTC
  • Shugaba Rohani Ya Gana Da Ayatollahi Sistani

Shugaban jamhoriyar musulinci na Iran ya gana babban marja'in mabiyar mazhabar shi'a a kasar Iraki Ayatollahi sayyid Ali Sistani

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa a safiyar yau laraba, Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rohani ya kai ziyara gidan babban marja'in mabiya mazhabar shi'a na kasar Iraki Ayatollahi sayyid Ali Sistani inda ya gana tare da tattaunawa da shi, hakan kuwa na zuwa ne bayan ziyarar da ya kai hubbarin Imam Ali (a.s) imami na farko kuma khalifan Manzon Allah (s.a.w.a) ga mabiyar mazhabar iyalan gidan Anabta tsarkaka.

Tun a ranar Litinin din da ta gabata ce Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rohani  ya fara ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar ta Iraki, a yayin wannan ziyara shugaban ya gana da manya-manyan mahukuntan kasar gami da wasu kwararu na kasar ta Iraki.

Cikin tattaunawar da magabatan kasashen biyu suka yi, sun kula yarjejjeniyar aiki tare har guda biyar.

Ko baya ga hakan mahukuntan biyu sun amince da bayar da visa kyauta ga 'yan kasashen biyu, cikin wani bayanin hadin gwiwa da suka fitar a jiya talata.

Tags