Shugaba Hassan Rauhani Ya Kai Ziyara A Turkiyya
(last modified Thu, 20 Dec 2018 21:42:25 GMT )
Dec 20, 2018 21:42 UTC
  • Shugaba Hassan Rauhani Ya Kai Ziyara A Turkiyya

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya kai ziyarar aiki a yau a kasar Turkiya.

Shugaba Rauhani ya gudanar da  ziyarar ta yini guda a yau a kasar Turkiya, inda ya gana da takwaransa na Turkiya Rajab Tayyib Erdogan, kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Sa'annan kuma an sanya hannu kan wasu muhimman yarjeniyoyi na bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayya na biliyoyin daloli tsakanin Iran da Turkiya.