Komitin Tsaro Na MDD Ya Fara Zama Kan Yerjejeniyar Nukliyar Kasar Iran.
A dazu-dazun nan ne komitin tsaro na MDD ya fara zama don sauraron rahoton dangane da yerjejeniyar Nukliyar kasar Iran, wacce kudurin MDD ta 2231 ta maida ita doka.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gotteres ne yake gabatar da rahoto danagne da yerjejenioyar a zaman komitin na yau Laraba.
A shekara ta 2015 ne komitin tsaro na MDD ta amince da wannan yerjejeniyar, inda dukkan membobin majalisar 15 suka amince da ita sannan aka samar da kuduri mai lamba 2231 ya maida ita doka.
Kudurin na 2231 dai ya bukaci babban sakataren majalisar dinkin duniya ya gabatar da rahoto kan yerjejenioyar a ko wani watanni 6.
Ya zuwa yanzu dai hukumar IAEA mai kula da harkokin makamshin nukliya a duniya ta bada rahotanni fiye da 6 kan cewa kasar Iran tana cika alkawarinta da ta dauka a yerjejeniyar.
Wasu rahotannin sun bayyana cewa sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya halarci zaman komitin tsaron da kansa don nanata zargin ta Amurka takewa Iran kan shirinta na makamai masu linzami.