Mali : MDD, Ta Damu Kan Kasa Aiwatar Da yarjejeniyar Zaman Lafiya
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna matukar damuwarsa akan tsaikon da ake fuskanta wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya 2015 da aka cimma tsakanin bangarori a kasar Mali.
Duk da cewa kasashe mambobin kwamitin sun yaba da kokarin da fira ministan kasar ta Mali keyi wajen karfafa yarjejeniyar, amma suna kira ga sauren bangarorin da batun ya shafa dasu hada karfi da karfe bayan sake zaben shugaba Ibrahim Boubakar Keita domin yi aiki tare na karfafa wa yarjejeniyar wajen tabbatar da zaman lafiya mai daurewa da kuma 'yancin dan adam.
A hannu guda kuma kasashen mambobin kwamitin sun bukaci gwamnatin Mali da kuma gungun masu dauke da makamai da masu ruwa da tsaki kan batun dasu dauki kwararen matakai cikin gaggawa na ganin an kai ga cimma sauren batutuwa masu mahimmanci da yarjejeniyar ta tanada.
Batun ajiye makamai da kuma samar da yankuna masu cin gashin kansu na daga cikin batutuwan da har yanzu ba'a kai ga warware su ba, kamar yadda sanarwar bayan taron da kwamitin tsaron MDD, ya gudanar kan kasar ta Mali.