Mali : Mata Da Diyan Sojoji Sunyi Zanga zanga
(last modified Sat, 23 Mar 2019 06:19:27 GMT )
Mar 23, 2019 06:19 UTC
  • Mali : Mata Da Diyan Sojoji Sunyi Zanga zanga

A Kasar Mali, ‘yan uwa da mata da kuma diyan sojojin kasar ne sukayi zanga zanga a biranen Segu da Sevare dake tsakiyar kasar domin nuna bacin ransu akan yawaitar kashe kashen sojojin kasar a hare haren ta'addanci.

Mata da diyan sojojin sun kuma nemi gwamnati kasar data dauki kauraren matakai ciki harda samar da kayan aiki ga sojojin kasar, a yakin da suke da mayakan dake ikirari da sunan jihadi da 'yan tada kayar baya.

Ko a ranar 17 ga watan Maris, sojojin kasar 26 ne suka rasa rayukansu a wani hari a yankin Dioura dake tsakiyar kasar.

A halin da ake ciki dai gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku daga jiya Juma'a domin juyayin sojojin da suka rasa rayukansu a mummunan harin na Dioura.

 

Tags