-
Jami'an Tsaron Iran Sun Sami Nasarar Tarwatsa Wasu Kungiyoyin 'Yan Ta'adda Biyu A Tehran
May 29, 2018 01:17Kwamandan sansanin Muhammad Rasulallah na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da ke birnin Tehran ya sanar da cewa dakarun kare juyin sun sami nasarar tarwatsa wasu kungiyoyin 'yan ta'adda da suke shirin kai hare-hare birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
-
Iran Ta Karyata Labarin Cewa Tana Tattaunawa Da H.K.Isra'ila
May 29, 2018 01:17Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, ya musanta labarin da wasu suke yadawa na cewa Iran tana tattaunawa ta bayan fage da haramtacciyar kasar Isra'ila a kasar Jordan.
-
Iran: Amurka Da H.K.Isra'ila Gami Da Saudiyya Suke Tada Hankali A Yankin Gabas Ta Tsakiya
May 28, 2018 01:57Mai bada shawara ta musamman ga shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya bayyana cewa: Kasar Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila gami da 'yar koransu Saudiyya ce suke goyon bayan ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya.
-
Shamkhani: Iran ZA Ta Ci Gaba Da Taka Rawa A Siriya Da Kuma Goyon Bayan Gwargwarmaya
May 27, 2018 13:25Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Shamkhani ya bayyana cewar Iran za ta ci gaba da taka rawar da take takawa a Siriya da kuma ci gaba da goyon bayan kungiyoyin gwagwarmayar duk kuwa da bukatar kawo karshen hakan da Amurka ta gabatar mata.
-
Iran Ta Ce: Sakataren Harkokin Wajen Kasar Amurka Ya Jahilci Yadda Duniya Ta Sa Gaba
May 26, 2018 13:37Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya fayyace cewa: Hakkin kasar Iran ne tace sinadarin yuraniyom kuma tana da kwararrun masana da suke da wannan fasahar.
-
Duk Tare Da Takunkuman Amurka Kan Gwamnan Babbam Bankin Iran Hukumar Lamuni Ta Duniya Zata Yi Aiki Da Shi
May 26, 2018 02:05Hukumar bada lamuni ta duniya The International Monetary Fund (IMF) ta bada sanarwan cewa zata ci gaba da aiki tare da gwamnan babbam bankin Iran Waliyullah Saif duk tare da takunkuman da gwamnatin Amurka ta dora masa.
-
Taron Kwamitin Kasashen Da Suka Rage A Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
May 25, 2018 13:13Kwamitin kasashen da suak rage a yarjejeniyar nukiliyar Iran, ya kawo karshen wani zamansa a birnin Vienna, wanda shi ne irinsa na farko tun bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar da aka cimma da Iran a 2015.
-
Rouhani: Matukar Muka Kaskantar Da Kanmu Ga Masu Tinkaho Da Karfi, To Babu Inda Za Mu Kai
May 25, 2018 00:57Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewa duk wata al'umma da ta kaskantar da kanta ga masu tinkaho da karfi na duniya,to kuwa babu inda za ta je komai dukiyar da take da ita kuwa.
-
Qassemi: Zarge-Zargen Kasar Moroko Kan Iran, Wani Kokari Na Faranta Ran Wata Kasa
May 25, 2018 00:56Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, ya bayyana cewar: Ci gaba da maimaita tuhumce-tuhumcen karya da kasar Moroko ta ke yi kan Iran, wani lamari ne maras tushe wacce take yin hakan don faranta ran wata kasa ta daban ce.
-
Jagora: Dole Turawa Su Ci Gaba Da Sayan Man Fetur Na Iran Idan Suna Son Iran Ta Ci Gaba Da Mutunta Yarjejeniyar Nukliya
May 24, 2018 14:45Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a nan Iran ya bayyana wasu sharudda wadanda turawa zasu cika su kafin Iran ta ci gaba da mutunta yerjejiniyar shirin Nukliyar kasar da su.