-
Shugaban Iran Ya Kama Hanyar Halattar Zaman Taron Kungiyar O.I.C A Turkiyya
May 18, 2018 07:26Shugaban kasar Iran ya kama hanyar tafiya zuwa kasar Turkiyya domin halattar zaman taron kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta O.I.C kan matsalar Palasdinu.
-
Kamfanoni Kasar Jamus 120 Da Sauke Ayyukan Daban-Daban A Kasar Iran Zasu Ci Gaba Da Ayyukansu
May 18, 2018 01:58Ministan harkokin tattalin arziki na kasar Jamus ya bada sanarwan cewa kamfanonin kasar Jamus 120 da suke aiyuka daban da bana a kasar Iran zasu ci gaba da ayyukansu duk tare da janyewar Amurka daga yereheniyar shirin Nukliyar kasar Iran.
-
Kasashen Turai Zasu Dakatar Da Sayan Man Fetur Na Kasar Iran Da Dalar Amurka
May 18, 2018 01:56A daidai lokacinda gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa zata dakatar da amfani da dalar Amurka a duk wani hulda da take da kasashen waje, tarayyar turai ta ce kasashen kungiyar zasu rika sayan man fetur na kasar Iran da kudaden Euro maimakon dalar Amurka.
-
Rouhani Ya Kirayi Kasashen Musulmi Da Su Kalubalanci Aika Aikan Amurka Da 'Isra'ila' Kan Palastinawa
May 17, 2018 01:09Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana kisan gillan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta ke yi wa Palastinawa a matsayin babban bala'i inda ya kirayi shugabanni da kuma cibiyoyin kasashen musulmi da su kalubalancin irin wannan danyen aikin da 'Isra'ilan' bisa goyon bayan Amurka ta ke yi.
-
Tarayyar Turai Ta Bayyana Shirye-Shiryenta Na Ci Gaba Da Mutunta Yerjejeniyar Nukliyar Iran
May 16, 2018 14:50Shafin yanar gizo na tarayyar Turai ya bada bayanai dangane da yadda kasashen kungiyar zasu ci gaba da aiki da kasar Iran bisa yerjejeniyar da suka cimma da ita bayan ficewar kasar Amurka daga yerjejeniyar a makon da ya gabata.
-
Salehi: Iran Tana Da Karfin Komawa Kan Shirin Nukiliyanta Yadda Yake Kafin Yarjejeniya
May 15, 2018 12:18Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Iran Dakta Ali Akbar Salehi ya bayyana cewar: Matukar dai ba a lamunce wa Iran bukatunta ba, Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da karfin komawa ga matakin da take kai kafin yarjejeniyar nukiliya, har ma sama da hakan.
-
Gwamnatin Iran Ta Yi Allah Wadai Da Danyen Aikin Baya-Bayan Nan Na 'Isra'ila' Kan Palastinawa
May 15, 2018 12:16Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da kakkausar suka ga aika-aikan da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi kan Palastinawan Gaza, kamar yadda kuma ta bukaci kasashen duniya da su kawo karshen shirun da suke yi kan aika-aikan 'Isra'ilan' da kuma kokari wajen kawo karshen mamayar da ake yi wa Palastinawa.
-
Rasha : Putin Ya Gana Da Shugaban Hukumar IAEA
May 14, 2018 14:31Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gana da shugaban hukumar kula da harkokin makamashin Nukliya ta duniya Yokiyo Amano a birnin Mosco inda ya jaddada matsayin kasar Rasha na mutunta yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran.
-
Iran Ta Yi Allawadai Da Harin Ta'addancin Da Aka Kai A Birnin Paris
May 14, 2018 02:43Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya bayyana harin da aka kai a birnin Paris da cewa: aiki ne na ta'addanci, kuma Iran tana yin Allawadai da shi.
-
Jagora: Ya Zama wajibi Kan Kasashen Asia Su Kara Karfafa Hulda Da Junansu
May 14, 2018 02:37A yammacin jiya ne shugaban kasar Sri Lanka Maithripala Sirisena ya ziyarci jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a Tehran, a ziyarar da yake gudanarwa a kasar Iran.