May 18, 2018 06:28 UTC
  • Kamfanoni Kasar Jamus 120 Da Sauke Ayyukan Daban-Daban A Kasar Iran Zasu Ci Gaba Da Ayyukansu

Ministan harkokin tattalin arziki na kasar Jamus ya bada sanarwan cewa kamfanonin kasar Jamus 120 da suke aiyuka daban da bana a kasar Iran zasu ci gaba da ayyukansu duk tare da janyewar Amurka daga yereheniyar shirin Nukliyar kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Peter Altmaier ministan tattalin arziki da makamashi na kasar Jamus yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa a cikin tattaunawan da kasashen biyu zasu gudanar nan gaba a cikin wannan shekara zasu kara bayyana hanyoyuyin karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

A nashi bangaren ministan makamashi na kasar Iran Razi Ardekaniyyan ya bayyana cewa kasashen Iran da Jamus sun amince kan gudanar da taro na komitin tattalin arziki na kasashen biyu nan gaba a wannan shekara, duk da cewa har yanzun ba'a bayyana lokacin taron ba. 

Riza Ardekaniyyan wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar ta Jamus ya bayyana cewa komitin tattalin arziki na kasashen biyu yana da sassa na makamashi da ruwa, tattalin arziki da kuma kyautata yanayi, kuma zasu ci gaba da aiki tare don kawo ci gaba ga bangarorin biyu.

 

Tags