Mar 07, 2019 04:37 UTC
  • Gwamnatin Venezuela Ta Kori Jakadan Jamus A Kasar

Gwamnatin Shugaba Nicolas maduro na kasar Venezuela ta sanar da korar jakadan kasar Jamus, daga kasar.

Sanarwar da gwamnatin venezuela ta fitar, ta ce an baiwa jakadan na Jamus, Daniel Kriener, wa'adin sa'o'i 48 na ya bar kasar, saboda shishigi a cikin al'amuran cikin gidan kasar.

Jakadan na Jamus na daga cikin jakadun kasashen waje dake birnin Caracas da suka tarbi jagoran 'yan hammaya na kasar ta Venezuela wanda ya ayyana kansa shugaban kasa cewa da Juan Guaido, a filin jirgi Caracas bayan dawowa daga ziyarar da ya kai a wasu kasashen yankin.

Sanarwar dai bata fayyace ko matakin ya shafi sauren jakadun kasashen wajen da suka tarbi Mista Juan Guaidon ba.

Jakadun kasashen waje 12 ne dai suka tarbi M. Guaido a lokacin da ya dawo daga ran gadin.

Mista R. Guaido ya bayyana matakin na gwamnatin Maduro da cewa ya barazana ce ga 'yancin walwala a duniya.

Tags