Mar 20, 2019 05:45 UTC
  • Iran Da Rasha Sun Tattauna Akan Kasar Venezuela

Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Rasha sun tattauna ta wayar tarho akan halin da kasar Venezuela take ciki.

Ma’aikatar harkoikin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa; Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bijiro da matsalar siyasar da kasar Venezuela take ciki a tattaunawar da ya yi da takwaransa Sergey Lavrov a  jiya Talata.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; Bangarorin biyu sun cimma matsaya akan taimakawa kokarin da kasashen duniya suke yin a ganin an warware matsalar kasar ta Venezuela.

Majiyar kasar Rashan ta kuma ce kasashen biyu sun kuma cimma matsaya akan yadda za su bunkasa alaka a tsakaninsu.

Dambaruwar siyasa ta fara ne a kasar Venezuela tun daga lokacin da jagoran ‘yan hamayya Juido Gaido kuma shugaban Majalisar Dokoki ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa.

Kasar Amurka da tarayyar turai sun nuna goyon bayansu ga jagoran ‘yan adawar, yayin da kasashen Iran, Rasha, da China suke goyon bayan shugaba Nicolas Maduro.

 

Tags