Mar 05, 2019 05:00 UTC
  • Daruruwan Mutanen Kasar Venezuela Sun Tsallaka Iyakar Kasar Zuwa Kasashe Makobta.

A dai-dai lokacinda rikicin kasar Veneziela ke kara tsanani , daruruwan mutanen kasar sun fara tsallakawa zuwa kasashe makobta.

Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ya bayyana cewa an ga daruruwan mutanen kasar suna ketara kogin Tachira na kan iyakar kasar da kasar Colombia, kusa da ofishin kan iyaka na kasashen biyu da ke Cucuta a ranar Litinin.

Wasu hotunan Bidiyo sun nuna masu tsallaka kan iyakar suna dauke da katifi da akwatuna da kuma sauran kayakin bacci.

Tun cikin watan Jenerun da ya gabata ne aka fara rikici a kasar Venezuela bayan da Juan Guaido ya shelanta kansa a matsayin shugaban kasar Venezuela na riko, inda kuma ya sami goyon bayan Amurka, kasashen Turai da kuma wasu kasashen yankin.

 

Tags