-
Shugaba Ruhani Ya Mayar Da Martani Ga Jawabin Shugaban Amurka Kan Iran
Oct 14, 2017 02:19Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar babu wani abu cikin jawabin shugaban Amurka Donald Trump kan Iran face wauta da tuhumce-tuhumce marasa tushe yana mai cewa al'ummar Iran ba za su taba mika wuya ga wani mai takama da karfi da girman kai ba.
-
Limamin Juma'a Na Tehran: Wajibi Ne Jami'an Gwamnatin Su Yi Caga Da Tsayin Daka Wajen Kalubalantar Amurka.
Oct 13, 2017 09:04Ayatullahi Muhamad Ali Muwahhadi Karmani ya ci gaba da cewa; Daukar darussa daga tarihi shi ne abinda ya kamata jami'an gwamnatin suyi wajen fuskantar girman kan Amurka.
-
Ministan Tsaron Iran Ya Gargadi Trump Kan Sanya IRGC Cikin Kungiyoyin Ta'addanci
Oct 12, 2017 13:53Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Amir Hatami ya jan kunnen shugaban Amurka Donald Trump dangane da sanya dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC) cikin kungiyoyin 'yan ta'adda yana mai cewa yin hakan ba abin da zai haifar in ban da kara zaman dardar da kuma yaduwar ta'addanci a yankin Gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.
-
Jami'an Tsaron Iran Sun Dakile Kokarin 'Yan Ta'adda Na Kai Hare-Hare Lokacin Ashura
Oct 10, 2017 02:22Ministan tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na kasar Iran Sayyid Mahmoud Alawi ya bayyana cewar jami'an tsaron Ma'aikatar tasa sun sami nasarar dakile wani shiri na kai hare-haren ta'addanci a cikin Iran lokacin Ashura yana mai cewa jami'an tsaron sun kame wani adadi na 'yan ta'addan.
-
Janar Jafari da Zarif Sun Mayar Da Martani Kan Kokarin Amurka Na Bata Sunan Dakarun IRGC
Oct 10, 2017 02:21Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluci na Iran (IRGC) Manjo Janar Muhammad Ali Jafari ya bayyana cewar bakin dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran da na Ma'aikatar harkokin wajen kasar sun zo daya a fagen kare manufofin juyin juya halin Musulunci yana mai kiran shugaban Amurka da ya fahimci hakan.
-
Dakarun Kare Juyi Na Iran Za Su Dau Sojojin Amurka Tamkar 'Yan Da'esh Idan Aka Sa Musu Takunkumi
Oct 08, 2017 13:35Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari ya bayyana cewa dakarunsa za su dauki sojojin Amurka tamkar 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh matukar dai Amurka ta sanya takunkumi da bata sunan dakarun nasa.
-
Kwamitin Zartarwar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Ya Gudanar Da Zama A Kasar Iran
Oct 07, 2017 15:39Kwamitin Zartarwar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ya gudanar da zamansa karo na 38 a birnin Tehran na kasar Iran a yau Asabar.
-
Babu Tattaunawa Kan Shirin Makamai Masu Linzami Na Kasar Iran
Oct 07, 2017 03:13Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa babu wata tattaunawa kan shirin makamai masu linzami na kasar Iran da kowace kasa a duniya.
-
Limamin Juma'ar Tehran: Amurka Ta Gama Karya Yejejeniyar Nukiliya
Oct 06, 2017 14:40Ayatullah Ahmad Khatami waanda yake magana akan matsayar Amurka danagne da yarjejeniyar Nukiliyar, ya ce; Babu wani abu da ya saura da Amurkan ba ta take ba.
-
Iran : Babu Zancen Sake Tattauna Yarjejeniyar Nukiliya_Salehi
Oct 06, 2017 07:32Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran, Ali Akbar Salehi, ya bayyana cewa, ba za a sake cimma wata sasantawa game da yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma tsakanin manyan kasashen duniya.