Babu Tattaunawa Kan Shirin Makamai Masu Linzami Na Kasar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i24709-babu_tattaunawa_kan_shirin_makamai_masu_linzami_na_kasar_iran
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa babu wata tattaunawa kan shirin makamai masu linzami na kasar Iran da kowace kasa a duniya.
(last modified 2018-08-22T07:00:48+00:00 )
Oct 07, 2017 03:13 UTC
  • Babu Tattaunawa Kan Shirin Makamai Masu Linzami Na Kasar Iran

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa babu wata tattaunawa kan shirin makamai masu linzami na kasar Iran da kowace kasa a duniya.

Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Bahram Qasimi yana fadar haka a jiya jumma'a a lokacin da yake maida martani kan wani labari wanda kamfanin dillancin labaran reuters ya watsa na cewa Iran a shirye take ta tattaunawa kan makamanta masu linzami.

Qasimi ya kara da cewa jumhuriyar Musulunci ta Iran ta sha nanatawa, kuma ministan harkokin wajen kasar ya sha fada, ya kuma nanata a birnin New York na kasar Amurka a baya bayan nan kan cewa shirin makaman tsaron kasar Iran ba abin tattaunawa akai ba ne, kuma tattaunawa a kansa ya saba wa kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231 wacce ta tabbatar da yerjejeniyar da ta ta cimmma da manya manyan kasashen duniya.

Banda haka hatta kakakin ma'aikatar harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Nabila Massrali ta bayyanan cewa shirin makamai masu linzami na kasar Iran da kuma gwaje-gwajen ta take gudanarwa ba su saba wa kudurin MDD mai lamab 2231 ba.