-
Salihi:Babu Sabuwar Tattaunawa Kan Shirin Nukliyar Iran
Oct 05, 2017 13:23Shugaban hukumar Makamashin nukliya na kasar Iran Ali Akbar Salihi ya bayyana cewa babu wata sabuwar tattaunawa kan shirin makamashin nukliyar kasar.
-
Jagora: H.K.Isra'ila Tana Kokarin Sake Samar Da Wata Sabuwar Isra'ila Ce A Yankin Gabas Ta Tsakiya
Oct 05, 2017 04:00Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya fayyace cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana kokarin sake samar da wata sabuwar Isra'ila ce a yankin gabas ta tsakiya, don haka take ingiza Kurdawa kan raba kasar Iraki.
-
Shugabannin Iran Da Turkiyya Sun Bayyana Rashin Amincewa Da Rarraba Kasar Iraki
Oct 04, 2017 13:52Shugabannin kasashen Iran da Turkiyya sun bayyana cewa ba za su taba amincewa da kokarin Kurdawa na rarraba kasar Iraki ba, suna masu sake jaddada shirin gwamnatocinsu na kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
-
Turkiyya / Iran : Erdogan Na Ziyara A Tehran
Oct 04, 2017 07:27Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya fara wata ziyara aiki a nan birnin Tehran na Jamhuriya musulinci ta Iran, inda ya gana da takwaransa na Iran din Hassan Rohani.
-
Iran Ta Mika Sakon Ta'aziyarta Kan Rasuwar Tsohon Shugaban Kasar Iraki Jalal Talibani
Oct 03, 2017 15:32Ministan harkokin wajen kasar Iran ya aike da sakon ta'aziyya ga gwamnatin Iraki da al'ummar kasar kan rasuwar tsohon shugaban kasar Jalal Talibani.
-
Zarif: Iran Tana Da Zabi Masu Yawa Idan An Sabawa Yerjejeniyar Nukliya Da Ta Kulla
Oct 03, 2017 03:15Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zareef ya bayyana cewa JMI tana da zabi masu yawa idan kasar Amurka ta bayyana ficewarta daga yerjejeniyar Nukliya da aka kulla ta ita a shekara ta 2015.
-
Mutanen Lardin Catalonia Sun Yi Zanag-Zangar All..Wadai Da Yansandan Kasar
Oct 03, 2017 03:14Dubban daruruwan mutanen yankin catalonia masu son ballewa daga kasar Espania sun gudanar da zanga zanga inda suke yin All..wadai da yadda yan sanda suke yi kokarin hana mutanen yankin gudanar da zaben raba gardama da karfi.
-
Kasashen Iran Da Turkiyya Sun Karfafa Matakan Tsaro A Iyakokinsu
Oct 02, 2017 13:11Kasashen Turkiyya Da Iran sun karfafa matakan ayyukan soji a wani mataki na tsaron iyakokinsu.
-
Juyayin Ashura Ya Game Dukkan Yankunan Kasar Iran A Yau Lahadi
Oct 01, 2017 15:46An gudanar da juyayin ashoora a duk fadin Iran a yau Lahadi wanda yayi dai dai na 10 ga watan Muharram ranar tunawa da shahadar Imam Husain (a) jikan manzon All..(s).
-
Jawad Zarif: Neman Ballewar Yankin Kurdawan Kasar Iraki Barazana Ce Ga Zaman Lafiyan Yankin
Oct 01, 2017 03:03Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Zaben neman ballewar yankin Kurdawan Iraki daga kasar babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yankin gabas ta tsakiya.