Mutanen Lardin Catalonia Sun Yi Zanag-Zangar All..Wadai Da Yansandan Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i24571-mutanen_lardin_catalonia_sun_yi_zanag_zangar_all..wadai_da_yansandan_kasar
Dubban daruruwan mutanen yankin catalonia masu son ballewa daga kasar Espania sun gudanar da zanga zanga inda suke yin All..wadai da yadda yan sanda suke yi kokarin hana mutanen yankin gudanar da zaben raba gardama da karfi.
(last modified 2018-08-22T11:30:46+00:00 )
Oct 03, 2017 06:44 UTC
  • Mutanen Lardin Catalonia Sun Yi Zanag-Zangar All..Wadai Da Yansandan Kasar

Dubban daruruwan mutanen yankin catalonia masu son ballewa daga kasar Espania sun gudanar da zanga zanga inda suke yin All..wadai da yadda yan sanda suke yi kokarin hana mutanen yankin gudanar da zaben raba gardama da karfi.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewa masu zanga zangar sun bayyana goyon bayansu ga zaben raba gardaman da kuma bellewar yankin daga kasar ta Espania bayan an kammala kada kuri'ar raba gardamar.

Duk da cewa gwamnatin kasar Espania ta haramta zaben raba gardaman ta kuma bayyana cewa zaben bai da halacci ko an gudanar da ita hakama babban kotun kasar ta bayyana zaben kan cewa baya bisa doka amma an gudanar da wannan zaben a ranar Lahadin da ta gabata kuma miliyoyin mutanen yankin sun foti don kada kuri'unsu. Majiyar wadanda suka shirya zaben a birnin Basaloli babban birnin yankin sun bayyana cewa kashi 90% na musu kada kuri'a sun amince da bellewar yankin.