Dec 28, 2018 06:41 UTC
  • Firai Ministan Kasar Espania Yana Ziyarar Aiki A Kasar Mali

Fira Ministan kasar Espania yana ziyarar aiki a kasar Mali, inda ake saran zai gana da sojojin kasar wadanda suke aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Kamfanin dilancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa, Pedru Sonchize ya isa kasar Mali sannan ana saran bayan ganawarsa da sojojin kasar wadanda suke zaune a wani sansaninsu da ke tazarar kilomita 60 daga birnin Bamako babban birnin kasar, zai gana da tokoransa na kasar Mali Sumaila Bubeye Maiga. 

Sojojin kasar Espania dai suna aikin horas da sojojin kasar Mali ne a karkashin shirin nan na tarayyar turai ta EUTM. Ofishin Firai ministan na kasar Espania ya bayyana cewa ziyarar ta jinjinawa sojojin kasar da suka aiki a kasar ta Mali da kuma duba irin halin da suke ciki.

Kasar Mali dai tana fama da tashe tashen hankula tun bayan wani juyin mulki wanda sojoji suka aiwatar a kasar a shekara ta 2012.

Sai kuma daga baya kungiyoyin yan ta'adda suka bulla a arewacin kasar wadanda suka zama barazana ga tsaron kasashen yankin.

Tags