Jan 06, 2019 17:00 UTC
  • An Kubutar Da Bakin Haure 550 Daga Halaka A Tekun Medeterenian

Jami'an tsaron ruwa na kasar Italiya sun bada labarin kubutar ta bakin haure kimani 550 daga halaka a cikin tekun Medeterenina.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto wata majiyar jami'an tsaro na ruwa a kasar Italiya tana fadar haka. Ta kuma kara da cewa a yau Lahadi ne suka kubutar da bakin haure 199 wadanda suke cikin wasu kananan kwale-kwale 5 daga gabacin Jabal Tarik, sannan a jiya Asabar kuma suka kubutar da wasu bakin hauren 350 wadanda suke cikin kananan kwale-keali 6 su ma kusa da jabal Tarik. 

A cikin wadanda aka kubutar dai akwai yara kanana 4 da kuma tsoffi 10. Sauran kuma matasa. Hukumar yan gudun hijira ta MDD ta bada sanarwan cewa a cikin shekara da ta gabata yan gudun hijira ko bakin haure 2262 suka rasa rayukansu a cikin tekun medeterenina. 

Tags