Salihi:Babu Sabuwar Tattaunawa Kan Shirin Nukliyar Iran
Shugaban hukumar Makamashin nukliya na kasar Iran Ali Akbar Salihi ya bayyana cewa babu wata sabuwar tattaunawa kan shirin makamashin nukliyar kasar.
Salihi ya bayyana haka ne a yau Alhamis a wata hira da muryar jumhuriyar musulunci ta Iran a yau Alhamis a birnin Roma na kasar Italia inda ya ke halartar wani taron kasa da kasa. Shugaban hukumar yana maida martani ne ga wasu manya manyan jami'an gwamnatin kasar Amurka wadanda suka bukaci a sake sabuwar tattaunawa kan shirin nukliyar kasar ta iran.
Salihi ya kara da cewa idan gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yerjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da kasahe 5+1 a shekarata 2016 to komitin da aka kafa a nan Iran don kula da lamuran yerjejeniyar ne zai fayyace matakin da yakamata Iran ta dauka. Har'ila yau Salihi ya kara da cewa duk sauran kasashen da aka kulla wannan yerjejeniyar da su wato Britania, Faransa, Rasha, China da kuma Jamus sun tabbatar da cewa suna tare da yerjejeniyar kuma babu wani bukatar sake tattaunata.