Iran Ta Gargadi Kasashen Turai Game Da Yarjejjeniyar Nukiya.
(last modified Thu, 31 Jan 2019 07:30:09 GMT )
Jan 31, 2019 07:30 UTC
  • Iran Ta Gargadi Kasashen Turai Game Da Yarjejjeniyar Nukiya.

A yayin da kungiyar tarayyar turai ke da'awar cewa nan ba da jimawa ba za ta samar da wata hanyar saukaka mu'amalar kasuwanci da kasar Iran, hukumomin birnin Tehran sun gargadi kungiyar da rashin cika alkawari.

A yayin da yake tattaunawa da tashar talabijin din Rusiya Al-yaum mallakin kasar Rasha, kakakin ma'aikatar harakokin wajen kasar Iran Bahram Qassemi ya ce idan kasashen Turai ba su cika alkawari ba, to shakka babu jamhoriyar musulinci ta Iran za ta sake nazari kan yarjejjeniyar nukiyar zaman lafiyar da ta cimmawa tare manyar kasashe 5 gami da kasar Jamus.

Ya zuwa yanzu dai kasashen na Turai sun yi ta bayar da wa'adin daban-daban na zartar da yarjejjeniyar da suka cimmawa da Iran, amma suna jinkirtawa, a wani sabon alkawari da ya fito daga kakakin shugabar harakokin siyasar wajen kasashen Turai a jiya Laraba, ta ce kokarin da kungiyar turai ke yi na samar da hanyar mu'amalar kasuwanci da kudi tare da kasar Iran yana matakin karshe.

Kimanin watani 9 kenan da kasar Amurka ta janye daga yarjejjeniyar da kasashen Amurka, Faransa, Rasha, Birtaniya, China gami da kasar Jamus suka cimmawa kan nukiliyar Iran na zaman lafiya, amma har yanzu kasashen na Turai na cewa suna cikin kokarin samar da wata hanya ce da za su kewaye kasar Amurkan su ci gaba da raya wannan yarjejjeniya, tare da yin alkawarin cewa za su samar da wani banki na musaman domin saukaka hadahadar kasuwanci da kudi tsakaninsu da jamhoriyar musulinci ta Iran.

Kungiyar EU ta ce matukar aka samar da wannan hanya, to takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa jamhoriyar musulinci ta Iran ba zai yi wani tasiri ba.domin nuna kyakkyawar niya , hukumomin kasar ta Iran sun bawa kasashen na Turai dama na samar da wannan hanya, amma a halin yanzu, Iran ta ce hakurinta ya kusa kawo karshe, domin amfanuwa da harakokin kasuwanci da kuma tattalin arziki na yarjejjeniyar nukiliyar zaman lafiyan da aka cimma, hakin Al'ummar Iran ne, matukar kuma kungiyar tarayyar Turai ta kasa aiki da alkawarin da ta dauka, hakin Iran ne ta sake yin nazari kan yarjejjeniyar.

Bahram Qassemi ya ce a halin da ake ciki, kasar Iran ta nuna kyakkyawar niyarta na aiki tare kasashen turai, yanzu kuma lokacin da kungiyar turai na dauka na zartar da shirin na dab da karewa.

Tajruba ta nuna cewa fitar Amurka daga cikin yarjejjeniyar nukiliyar da kasashen Iran ta Cimma da kasashe 5+1 da kuma irin alkawarin da kasashen Turai suka dauke na ci gaba da zartar da yarjejjeniyar ba tare da cikawa ba, dogaro da karfin cikin gida da kuma amfani da abubuwan da ake gyerawa cikin kasar, shi ne mafi dacewa ga al'ummar kasar ta Iran.

A kan haka ne, tsohon ministan harakokin wajen kasar ta Iran kuma shugaban Majalisar al'amuran da suka shafi kasashen wajen waje Kamal Kharazi a ranar Talatar da ta gabata ya ce duk da irin alkawarin da kasashen Turai suka dauka na samar da wani Banki na musaman da zai sawwake hadahadar kudi tsakanin Iran din da kasashen Turai to dale ne mu dogara da kanmu domin kare amfanin kasarmu.