Kasashen Iran Da Turkiyya Sun Karfafa Matakan Tsaro A Iyakokinsu
(last modified Mon, 02 Oct 2017 16:41:21 GMT )
Oct 02, 2017 16:41 UTC
  • Kasashen Iran Da Turkiyya Sun Karfafa Matakan Tsaro A Iyakokinsu

Kasashen Turkiyya Da Iran sun karfafa matakan ayyukan soji a wani mataki na tsaron iyakokinsu.

Bangarorin biyu sun bayyana hakan ne a yayin wata ganawa ta mayan hafsoshin sojin kasashensu yau Litini a nan Birnin Teheran.

ziyara da babban hafsan sojin kasar Turkiyya ya kawo a nan birnin Teheran a yau Litini.

Babban hafsan sojin kasar Iran Janar Mohammad Bakeri ya fada a wani taron manema labarai a yayain ganawa da takwaransa na Turkiyya Janar Hulusi Akar cewa kasashen biyu zasu karkafa ayyukan soji a iyakokinsu.  

Janar Bakeri ya kara da cewa ziyarar takwaransa wacce ta biyo bayan ziyara da ya kai a Turkiyya ta kara karfafa tsaro na kasashen biyu.

A daya bangare kuwa Janar Bakeri ya ce sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi bangarorin biyu wanda suka hada da barazana wasu kasashen ketare da yaki da ta'addanci da tsaron iyakokinsu inda dakarun kasashen biyu zasu dinga hadin gwiwa da kuma atisaye.

Akan batun zaben raba gardama na yankin Kurditan na Iraki kuwa, Janar Bakeri ya ce kasashensu suna kan bakarsu ta goyan bayan dunkulewar kasar Iraki guda tak.