Pars Today
Wasu majiyoyin labarai a kasar Siriya sun bayyana cewa sojojin kasar Britania 5 ne suka halaka a lokacinda yan ta'adda na kungiyar Daesh wadanda har yanzun suke iko da yankin Dair-Zur daga gabacin kasar suka cilla makamai masu linzami a kansu.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya isa a birnin Bagadaza na kasar Iraki, a wata ziyarar ba zata inda ya gana da wasu manyan jami'an kasar ta Iraki ciki harda shugaban majalisar dokoki.
Kafar watsa labaru ta Middle east ta Birtaniya ce ta buga labari da ke cewa an yi ganawar ne a tsakanin Yossi Cohen wanda shi ne shugaban kungiyar leken asirin haramtacciyar kasar Isra'ila, da takwarorinsa na kasashen Larabawan uku
Kakakin sojan kasar Yemen Yahya Sari'i ne ya bayyana cewa kawancen na Saudiyya ya keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a Hudaidah har sau 1924
Sojojin Rasha sun fara sintirin ne dai a daidai lokacin da kasar Turkiya take barazanar shiga cikin yankin Manbaj domin yakar rundunar kurdawa
Mike Pompao sakataren harkokin wajen kasar Amurka zai fara ziyarar aiki na kwanaki 7 zuwa kasashe 8 na yankin gabas ta tsakiya daga yau Talata.
Mutane akalla 5 ne suka rasa rayukansu a kauyen Umm Al-Hamam na yakin Qatif a kasar Saudiya a lokacinda jami'an tsaron kasar suka kai sumame a kan mutanen kauyen.
Babban sakataren jam'iyyar "Tunisian Legitimate Movement" ya yi maraba da shirin gwamnatin kasar na maida huldan jakadanci da kasar Siriya.
Asusun Kananan yaran na Majalisar Dinkin Duniyar ya sanar da cewa; Da akwai kananan yara 10,000 da suke cikin mawuyacin hali a sansanonin 'yan gudun hijira
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikciin Yemen Martin Griffith ya gana da jagoran kungiyar Ansarullah (Huthi) a birnin Sanaa fadar mulkin kasar Yemen.