An Yi Maraba Da Shirin Maida Huldar Jakadanci Da Kasar Siriya
Babban sakataren jam'iyyar "Tunisian Legitimate Movement" ya yi maraba da shirin gwamnatin kasar na maida huldan jakadanci da kasar Siriya.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Muhsin Marzuq yana fadar haka a birnin Tunis. Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Tunisia tana maraba da ziyarar shugaban Bashar Al-Asad na Siriya zuwa kasar Tunisia a duk lokacinda ya shirya.
Marzuq ya bayyana cewa mutanen kasar Siriya tare da sojojin kasar da kuma shugabansu sun sami nasara a kan yan ta'adda a kasar. Wannan nasarar ba karamin matsayi ne ga mutanen kasar ba.
Ya kuma bayyana cewa tuni shuwagabannin kasashen Larabawa sun fara ziyartar kasar, shugaban kasar Sudan shi ne shugaban kasashen larabawa da ya fara ziyartar kasar Siriya. Sannan sauran kasashen yankin suna sake bubbude ofisoshin jakadancinsu a birnin Damascus.