Mar 07, 2019 04:37 UTC
  • An Tsawaita Doka Ta Baci A Kasar Tunisia.

Shugaban kasar Tunisia Algaji Qa'ed Assibsi ya bada sanarwan tsawaita doka ta baci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban kasar yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa ya dauki wannan matakin ne bayan tattaunawa da Firai Ministan kasar Yusuf Ashaheed da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Muhammad Annasir.

Tun ranar 24 ga watam Nuwamban shekara ta 2015 ne dai aka kafa doka ta bashi a kasar ta Tunisia bayan yan da yan ta'adda suka kai hari kan wata motar Bus dauke da sojoji na musamman masu tsaron fadar shugaban kasa, inda mutane 12 suka mutu sannan wasu da dama suka ji rauni.

Tun lokacinne aka tsawaita wannan dokar a ko wace shekara, a wannan karon ma an tsawaita dokar ne har zuwa 07 ga watan Afrilu na shekara ta 2020.

Tags