Mar 07, 2019 04:47 UTC
  • An Sanar Da Ranakun Manyan Zabuka A Tunisia

Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar Tunisia ta sanar da ranar 6 ga watan Oktoba mai zuwa a matsayin ranar da za'a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar, a yayin da za'a gudanar da zaben shugaban kasa kuma a ranar 10 ga watan Nuwamba a cikin wannan shekara.

Za'a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, idan har ta kama makwanni biyu bayan zagayen farko, a cewar hukumar.

Wannan dai shi ne karo na biyu da al'ummar Tunusia zata kada kuri'a a manyan zabukan kasar tun bayan guguwar neman sauyin da ta yi gaba  da gwamnatin Zine el Abidine Ben Ali a cikin shekara 2011.

A shekara 2014 ne jama'ar Tunisia suka kada kuri'a bisa tafarkin demukuradiyya wanda kuma ya kawo Shugaba Béji Caïd Essebsi kan madafun iko.

Hukumar zaben kasar ta ce za tayi duk kokarinta na ganin an samu yawan masu kada kuri'a a zaben dake tafe, inda ka wo ya zuwa yanzu mutum miliyan 5.7 ne suka yi rejista a cikin miliyan 8.9 na jimillar wadanda suka cancanci yin zabe a kasar

 

Tags