Pars Today
Shugaban dakarun sa kai na Hashdu-Sha'abi a kasar Iraki ne ya bayyana haka a yayin mayar da martani akan kokarin da Amurka take yi na yi musu iyakar zirga-zirga a kusa da iyakar kasar Syria
A jiya Litinin ne sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila su ka bude wuta akan Palasdinuwa a kan iyaka da Gaza, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane 7 daga cikinsu
Majiyar tsaron kasar Syria ta ce; wasu abubuwa ne da ake zaton bama-bamai ne suka tashi a kusa da sansanin 'yan ta'addar kungiyar Tahrir-As-sham wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar fiye da mutane 50
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Poland ta kirayi jakadan Isra'ila a kasar domin nuna masa takaicin kasar kan irin kamalan da suka fito daga bakin ministan harkokin wajen Isra'ila na rikon kwarya Katsap.
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan rikicin Yemen Martin Griffiths ya gana da shugaban kungiyar Ansarullah Abdulmalik Badruddin Alhuthi a birnin San'a.
Shugaba Bashar Al-Assad, na Siriya ya bayyana cewa har yanzu da sauren aiki game da yakin da kasarsa ke fama dashi.
Majalisar Dinkin Duniya, ta sanar da cimma wata yarjejeniya tsakanin bangarorin dake rikici a Yemen, wacce ta tanadi janye masu dauke da makamai a birnin Hodeida.
Babban magatakardar kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi na ranar tunawa da jagororin gwagwarmaya da su ka yi shahada
Gwamnatin Amurka ta bada sanarwan cewa zata bukaci kawayenta su kawo daruruwan sojoji zuwa kasar Siriya bayan ta janya.
Kungiyoyin gwagwarmayar Falastine Hamas da Jihadul Islami sun yi Allawadai da harin ta'addancin da aka kai kan jami'an tsaron Iran a garin Zahidan.