Pars Today
Wato kotu a kasar Espania ta fara sauraron shari'ar shuwagabannin wadanda suke son ballewar yankin Cathalonia daga kasar Espania.
Wata mata musulmi sanya da hijabi kuma 'yar majalisar mai wakiltar wani yanki a birnin Geneva na kasar Swizland ta bayyana cewa ba zata ciri hijabinta ba sanadiyyar sakamakon zaben raba gardama da aka gudanar a ka batun.
Shekh Tamim bin Hamad Al Thani sarki Qatar ya aike da sakon murna ga shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran na cika shekaru 40 cib da cin nasarar juyin musulinci na kasar
Saktare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka kan matakin da wasu kasashe suka dauka na kin karbar bakin haure.
Mutum guda ne jami'an tsaro a kasar Haiti suka kashe a zanga-zangar tsadar rayuwa wanda mutanen kasar suka gudanar.
Sakamakon wasu tsare-tsaren jin ra'a yin da aka gudanar a kasar Faransa don magance zanga-zangar da masu kin jin tsarin jari hujja a kasar yana nuna cewa mafi yawan mutanen kasar suna goyon bayan zaben raba gardama.
Kasashen Amurka da Rasha na ci gaba da samun sabani kan rikicin kasar Venezuela, inda kasashen biyu suka gabatar da kudurorin doka mabambanta kan kasar a zauren kwamitin tsaro na MDD.
Shugabar Majalisar wakilan ta Amurka Nancy Pelosi ta bayyana Juan Guaido a matsayin shugaban kasar Venezuela
A Faransa, yau Asabar ma masu boren adawa da siyasar shugaban kasar, Emannuel Macron, kan haraji da gazawar gwamnati wajen biyan bukatun masu karamin hali da ya daganci tsadar rayuwa sun sake fitowa kan tituna.
Kafafen yada labarai na kasar Venezuela sun yada labarin tattaunawa ta waya kai tsaye wanda wani babban jami'an fadar shugaban kasar Amurka ya yi da sojojin kasar Venezuela inda suke kiransu zuwa ga juyin mulki a kasar.