Mafi Yawan Mutanen Faransa Suna Goyon Bayan Zaben Raba Gardama.
(last modified Sun, 10 Feb 2019 19:06:57 GMT )
Feb 10, 2019 19:06 UTC
  • Mafi Yawan Mutanen Faransa Suna Goyon Bayan Zaben Raba Gardama.

Sakamakon wasu tsare-tsaren jin ra'a yin da aka gudanar a kasar Faransa don magance zanga-zangar da masu kin jin tsarin jari hujja a kasar yana nuna cewa mafi yawan mutanen kasar suna goyon bayan zaben raba gardama.

Wani kamfani yan kasuwa mai suna IFOP a takaice ya bayyana cewa kashi 73% na muatnen kasar Faransa suna goyon bayan a gudanar da zaben raba gardama don kawo karshen rigimar da ake tayi tsakanin masu adawa da tsarin tattalin arzikin na shugaba Macron mai goyon bayan masu arziki. 

Wata majiyar ta bayyana cewa kashi 3/4 na mutanen kasar na goyon bayan zaben. 

Tuni dai an gabatar da wannan bukatar ga shugaba Emmanuel macron don amincewarsa. Idan har ya amince za'a guadanar da wannan zaben ne a ranar 26 ga watan Mayu na shekara ta 2019 da muke ciki tare da zaben majalisar dokokin tarayyar Turai. 

Banda haka rahoton jin ra'ayin ya nuna cewa kashi 58% na mutanen kasar Faransa basu yarda da siyasar shugaba Emmanuel Macron ba.