Sabani Tsakanin Rasha Da Amurka Kan Venezuela A Kwamitin Tsaro
(last modified Sun, 10 Feb 2019 10:23:37 GMT )
Feb 10, 2019 10:23 UTC
  • Sabani Tsakanin Rasha Da Amurka Kan Venezuela A Kwamitin Tsaro

Kasashen Amurka da Rasha na ci gaba da samun sabani kan rikicin kasar Venezuela, inda kasashen biyu suka gabatar da kudurorin doka mabambanta kan kasar a zauren kwamitin tsaro na MDD.

A kudirin data gabatar Amurka, ta bukaci kwamitin tsaro ya samar da hanyoyin taimakawa wajen shigar da kayan ayaji na kasa da kasa a Venezuela da kuma hanyoyin kaiwa ga shirya zaben shugaban kasa.

Kudirin na Amurka data amince da jagoran 'yan adawa na Venezuela a matsayin shugaban kasa, ya kuma bukaci babban sakatare na MDD, Antonio Guteress, da ya yi amfani da matsayin da yake dashi don gudanar da zabe a wannan kasar ta Venezuela, domin a cewarta kaucewa kara tabarbarewar al'amuran kasar.

Saidai Rasha wacce ke goyan bayan Shugaba Nicolas Maduro, ta gabatar da wani kudirin doka da ya yi hannun riga dana Amurka, inda ta bayyana matukar damuwa dangane da yadda Amurkar ke son yin amfani da karfi a rikicin cikin gida na kasar ta Venezuela. 

Rasha ta nemi da a shawo kan rikicin kasar ta Venezuela ta hanyar lumana, tare da goyan bayan dun hanyoyin da suka dace na samar da tattaunawa tsakanin 'yan kasar ta Venezuela.