-
MayakanTaliban sun kwace iko da wani yanki a Afghanistan
Mar 02, 2017 01:37Al'umma sun wayi gari da tashin bama-bamai a garin Baglan, abin da yayi sanadiyyar rasa rayuka da dama wanda suka hada da mata da kananan yara.
-
Sojojin Myanmar Sun Bayyana Kisan Musulmi A Matsayin Kare Dokar Kasa
Mar 01, 2017 15:34Rundunar sojin kasar Myanmar ta bayyana kisan kiyashin da take yia kan musulmi 'yan kabilar Rohingya a matsayin kare dokokin kasar da tabbatar da tsaro.
-
An Kashe Wani Ba'indiye A Amurka Bisa Zargin Cewa Musulmi Ne
Mar 01, 2017 15:33An bude wutar bindiga a kan wasu indiyawa guda biyu a cikin jahar Texas da ke kasar Amurka bisa zargin cewa su mabiya addinin muslunci ne.
-
Ministan Harkokin Wajen Faransa: Babu Alaka Tsakanin Ta'addanci Da Muslunci
Mar 01, 2017 15:20Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Marc Ayrault ya bayyana cewa, babu wata alaka a tsakanin addinin musulunci da ta'addanci.
-
MDD : Amina Mohammed Ta Yi Rantsuwar Kama Aiki
Mar 01, 2017 07:46An rantsar da Amina Mohammed, tsohuwar ministar muhalli ta Nigeria a matsayin mataimakiyar sakatare janar na MDD.
-
Kasar Siriya Ta Bayyana Cewa: Gwamnatin Turkiyya Tana Jigilar 'Yan Ta'adda Zuwa Cikin Kasarta
Mar 01, 2017 03:26Jakadan kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Gwamnatin Turkiyya ta tura 'yan ta'adda masu kafirta musulmi fiye da 300,000 zuwa cikin kasar Siriya da nufin kashe al'umma da rusa kasar.
-
Rasha Da China Sun Hau Kujerar Naki Kan Wani Kudurin Adawa Da Kasar Siriya A Kwamitin Tsaro
Feb 28, 2017 14:52Kasashen Rasha da China sun hau kujerar naki dangane da wani kudurin da kasashen Turai suka gabatar a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da zargin da suke yi na cewa gwamnatin kasar Siriyan ta yi amfani da makamai masu guba a kasar.
-
Tsohuwar Ministar Muhallin Nijeriya Ta Yi Rantsuwar Kama Aiki A Matsayin Mataimakiyar Babban Sakataren MDD
Feb 28, 2017 14:51Tsohuwar ministar muhalli ta Nijeriya Hajiya Amina Mohammed ta yi rantsuwar kama aiki a matsayin mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a bikin da aka gudanar a helkwatar MDDn da ke birnin New York.
-
A Yau Ne Kwamitin Tsaron MDD Zai Kada Kuri'a Kan Kara Kakaba Wa Syria Takunkumi
Feb 28, 2017 09:18Kwamitin tsaron majalisar dinkin na shirin gudanar da wani zama a yau domin kada kuri'a kan kakaba wa gwamnatin Syria wasu sabbin takunkumai, bisa zargin da wasu kasashen turawa suka mata na cewa ta harba makamai masu guba.
-
Adama Barrow Ya Sallami Babban Hafsan Hafsoshin Gambia
Feb 28, 2017 09:17Shugaban kasar ne Adama Barrow ya sallami babban hafsan hafsoshin sojin kasar Janar Ousman Badjie, tare da maye gurbinsa da Janar Masanneh Kinteh.