MDD : Amina Mohammed Ta Yi Rantsuwar Kama Aiki
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18126-mdd_amina_mohammed_ta_yi_rantsuwar_kama_aiki
An rantsar da Amina Mohammed, tsohuwar ministar muhalli ta Nigeria a matsayin mataimakiyar sakatare janar na MDD.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 01, 2017 07:46 UTC
  • MDD : Amina Mohammed Ta Yi Rantsuwar Kama Aiki

An rantsar da Amina Mohammed, tsohuwar ministar muhalli ta Nigeria a matsayin mataimakiyar sakatare janar na MDD.

A jawabinsa na maraba, da ita a jiya Talata sakatare janar na majalisar Antonio Guterres ya ce, ya yi matukar farin ciki da ta amince ta yi aiki da shi.

Da take ganawa da manema labarai Amina Mohammed ta ce, za ta mai da hankali wajen taimakawa sakatare janar din sake fasalin muradun ci gaba masu dorewa a majalisar.

Amina Mohammed ta kasasnce mace ta biyu 'yar Afrika da aka nada matsayin mataimakiyar sakatare janar na MDD.

Mace ta farko ita ce Asha-Rose Migiro, 'yar kasar Tanzania, wadda ta kasance kan mukamin daga 2007 zuwa 2012, karkashin shugabanci Ban Ki-moon