-
Akalla Mutane 6 Sun Mutu Sakamkon Wata Gagarumar Girgizar Kasa Da Ta Faru A Tsakiyar Kasar Italiya
Aug 24, 2016 00:44Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewar alal akalla mutane 6 sun rasa rayukansu kana wasu kuma sun sami raunuka, baya ga gine-ginen da suka rushe sakamakon wata gagarumar girgizar da ta faru da safiyar yau Laraba a tsakiyar kasar Italiya.
-
MDD Ta Nada Jami'in Bincike Mai Cin Gashin Kansa Kan Rikicin Kasar Sudan Ta Kudu
Aug 24, 2016 00:42Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya sanar da nada tsohon sojan kasar Holland Manjo Janar patrick Cammaert a matsayin jami'i mai gudanar da bincike kan rikicin da ya faru a birnin Juba, babban birnin kasar Sudan ta Kudu a watan Yulin da ya gabata lamarin da ya sake janyo rikici da zaman dardar na siyasa a kasar.
-
Mafi yawa daga cikin 'yan kasar Faransa na adawa da takarar Nicola Sarkozy
Aug 23, 2016 14:42Kusan kashi 80% na Al'ummar kasar Faransa na Adawa da sake tsayawar takarar Nicolas Sarkozy a zaben Shugabancin kasar na 2017 mai zuwa
-
Jakadan Siriya A MDD Ya Zargi Kasar Amurka Da Kawayenta Da Ruruta Wutan Yaki A Cikin Kasarsa
Aug 23, 2016 01:26Jakadan Kasar Siriya a Majalisar Dikin Duniya ya bayyana cewa: Jiragen saman yakin Amurka suna ci gaba da kashe fararen hula a kasar Siriya musamman mata da kananan yara da sunan kai hare-hare kan 'yan ta'adda.
-
Faransa : Sarkozy, Zai Tsaya Takara A Zaben 2017
Aug 22, 2016 11:04Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy ya bayyana anniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugabancin kasar na shekara 2017 dake tafe.
-
Kerry, Ya Bukaci Aikewa Da Dakarun MDD A Sudan Ta Kudu
Aug 22, 2016 10:38Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya jaddada bukatar aikewa da tawagar kiyaye zamen lafiya ta MDD wace zata kunshi dakarun Afrika a birnin Juba na Sudan ta Kudu inda gwabza kazamin fada a watan Yuli da ya gabata.
-
Amurka : Ci gaba Da Yin Suka Akan Halin Muguntar Jami'an Tsaro
Aug 22, 2016 07:20An gudanar da zanga-zang a birnin Newyork na Amurka domin nuna kin amincewa da halin muguntar 'yan sandan kasar.
-
Tunawa Da Ranar Da Sahyoniyawa Suka Sanya Wa Masallacin Kudus Wuta
Aug 22, 2016 01:08Ranar 21 ga watan Augustan 1969 ta kasance rana ce wacce ta shiga cikin tarihin irin aika-aikan da yahudawan sahyoniya suke ci gaba da yi wa bil'adama don kuwa rana ce da wani mai ra'ayin sahyoniyawan dan asalin kasar Australiya mai suna Denis Michael Rohan ya sanya wa masallacin Al-Aqsa alkiblar musulmi na farko kana kuma waje na uku mafi tsarki a wajensu, wuta; lamarin da ya kara fito da irin bakar aniyar sahyoniyawan.
-
Musulmin Singapore Sun Bukaci Sa-Ido Sosai A Manhajar Karatu A Makarantunsu
Aug 21, 2016 13:12Musulmin kasar Singapore sun bukaci sa-ido sosai kan tsarin manhajar koyarwa a makarantunsu, domin kauce wa yaduwar akidar takfiriyyar da ke haifar da ta'addanci a duniya da sunan jihadin mulsunci.
-
Jami'an Tsaron Jamhuriyar DR Congo Sun Kame 'Yan Tawayen Uganda 80 A Yankin Gabashin Kasar
Aug 19, 2016 13:23Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya sanar da kame gungun 'yan tawayen kasar Uganda da dama da suke da hannu a tashe-tashen hankula a yankin gabashin kasar.